Sayyid Abdulmalik badarudden al huthi shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen yace kasar Yamen tana shiri dare-da rana domin tunkarar yaki nan gaba da kasar Amurka da kuma Isra’ila kuma ya jaddada cewa mayakan kasar Masar ba za su mika makamansu ba kuma ba za su mika wuya ba.
Shugaban yayi wadanann kalaman ne a cikina jawabin da yayi a jiya jumaa, kuma yana zuwa ne kwana daya bayan da ministan dake kula da harkokin soji na HKI Isreal Katz yace za su ci gaba da daukar matakai kan kasashe daban-daban da suka hada da kasar Yamen da sauran kasashen larabwa dake nuna goyon bayan falasdinawa.
Haka zalika yayi gargadin cewa yin shiru a gaban Amurka da Isra’ila zai kara sanyawa zaluncinsu ya ci gaba da yaduwa ne a kasashen musulmi da na larabawa, don haka ya zama wajibi kowa ya shirya ya sadaukar da kai , yace Amerika ta kasa dakatar da mu duk da makaman da take takama da su da jiragen ruwa da sauransu, amma sun kasa dakatar da matakin soji da muka dauka don nuna goyon bayan alummar falasdinu .
Daga karshe shugaban na Ansarullah ya gargadi game da makircin Amurka da Isra’ila na canza tsarin gabas ta tsakiya , bayan kiran da Washington da tel aaviv suka na canza gabas ta tsakiya , don haka ya yi kira ga kasashen musulmi da larabawa da su tashi su kalubalanci wannan shiri mai makon su yi shiru suna kallo.