Ana Zaben Shugaban Kasa A Ghana

A Ghana yau ne al’ummar kasar suka kada kuri’a a babban zaben kasar. Mutum fiye da miliyan 18 ne suka yi rajistar zaben a cewar

A Ghana yau ne al’ummar kasar suka kada kuri’a a babban zaben kasar.

Mutum fiye da miliyan 18 ne suka yi rajistar zaben a cewar hukumar zaben kasar.

‘Yan takara 12 ne ke fafatawa a zaben na yau cikin har da ‘yan takarar indifenda biyu da mace guda, domin maye gurbin Shugaba Nana Akuffo Addo, wanda ke kammala wa’adinsa na biyu.

Fafatawar zata fi tsakanin mataimakin shugaban kasar Mahamudu Bawumia na jam’iyyar NPP, da tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama a karkashin jam’iyyar hamayya ta NDC.

Zaben na bana na daukar hankali kasancewar duka manyan ‘yan takara a zaben sun fito ne daga yankin arewacin kasar.

Batun tattalin arziki da tsadar rayuwa ne suka dabaibaiye yakin neman zaben.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments