A wani lokaci yau Litini ce ake fara tattauanwar neman tsagaita wuta a rikicin Sudan.
Gwamnatin Sudan din ta ce za ta tura tawaga birnin Alkahira domin yin tattaunawa da jami’an Amurka da na Masar, a yunkurin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe watanni 16 ana yi a kasar.
Gwamnatin mulkin sojin kasar, da ke yaki da rundunar bayar da daukin gaggawa (RSF), ta ce ba za ta halarci tattaunawar zaman lafiya a Switzerland ba sai an aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla a Jeddah.
Tattaunawar da Amurka ke jagoranta, wadda wakilan RSF suke halarta, tana neman kawo karshen yakin da ya barke a kasar a watan Afrilun 2023, tare da shawo kan bala’in rashin jinkai da ake fama da shi a Sudan wanda ya jefa ‘yan kasar kimanin miliyan 50 cikin tsananin yunwa.