Search
Close this search box.

Ana Sar Kotun ICC Za Ta Umarci Isra’ila Domin Dakatar Da Hare-Harenta A Gaza

Ana sa ran cewa Kotun Duniya Kan Hukunta Manyan Laifuka za ta umarci Isra’ila ta dakatar da munanan ruwan wutar da take yi a Gaza,

Ana sa ran cewa Kotun Duniya Kan Hukunta Manyan Laifuka za ta umarci Isra’ila ta dakatar da munanan ruwan wutar da take yi a Gaza, kamar yadda kafofin watsa labaran Isra’ila suka rawaito.

Masana shari’a sun bayyana cewa akwai yiwuwar kotun za ta ba da umarnin ranar Juma’a, kamar yadda wata majiyar diflomasiyyar Isra’ila ta shaida wa jaridar srael Hayom.

Ya ce kotun za ta iya ba da umarnin a dakatar da ayyukan soja da Isra’ila ke yi a Rafah ko ta nemi a tsagaita wuta a yaƙin da ake yi a Gaza ta hanyar umarnin kotu.

Wata ƙwararriya ta Majalisar Ɗinkin ɗuniya ta yi kira ga Isra’ila ta binciki zarge-zarga dama na cin zarafi da keta mutucin Falasɗinawa da ake tsare da su tun bayan harin 7 ga watan Oktoba da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar.

Wakiliyar Musamman ta Majalisar kan Cin Zarafi Alice Jill Edwards, ta faɗa a cikin wata sanarwa cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe na yadda ake lakaɗa wa mutane duka, da kulle mutane an rufe masu ido da kuma ɗaure musu hannaye na tsawon lokaci.

Babu martani nan take daga gwamnati ko sojojin Isra’ila kan zargin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments