Dan majalisar Amurkan mai suna Randall Adam Fine wanda yake wakiltar jam’iyyar “Republican” ya sake tunanowa duniya da yadda kasarsa Amurka ta jefa wa biranen Nagasaki da Hiroshima bama-baman Nukiliya a karshen yakin duniya na biyu, ta hanayr yin kira da a jefa wa zirin Gaza irin wadannan makaman na kare dangi.
Kungiyoyin Falasdinawa mabanbanta sun yi tir da wannan irin kira na ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kare dangi, suna masu yin kira ga ita kanta majalisar Amurka da ta fito da yi Allawadai da wannan kira wanda yake cike da kiyayya.”
Kungiyar Hamas ta bayyana abinda dan majalisar na Amurka ya yi da cewa, ya keta dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kamar kuma yadda yake a matsayin yin kira da a yi wa fiye da fararen hula miliyan daya kisan kiyashi.
Ita kuwa kungiyar jihadul-Islami ta bayyana cewa; Muna daukar kira irin wannan a matsayin yin zuga a fili da a tafka laifi akan bil’adama, sannan kuma abin kunya ne ga ita kanta majalisar Amurka wacce dama sun taba yi wa Bajemine Natanyahu tafi alhali shi ne mafi girman wanda ya tafka laifi aka bil’adama a wannan zamanin.
A nata bayanin, kungiyar “Popular Front” ta sanar da cewa; Kira irin wannan na a yi wa fararen hula kisan kiyashi b,a shi da banbanci da mafi munin laifukan da ‘yan Nazi su ka tafka.”