Eslami : duk wani mataki da Iran ta dauka ya dogara ne kan manufofi da muradun kasar

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami ya ce duk wanimataki da Tehran ta dauka ya dogara ne kan manufofi da muradun kasar. “Muna ci gaba bisa ga manufofinmu da bukatun kasa,” in ji Eslami Babban jami’in nukiliya na kasar Iran ya jaddada cewa daya daga cikin muhimman nasarorin juyin juya halin Musulunci […]

Rashin abinci mai gina jiki a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane 299

Ofishin yada labaran Gaza ya bayar da rahoton mutuwar Falastinawa 299 da suka fada cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki, da karancin kayan masarufi da magunguna. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera na cewa, taimakon jin kai na cikin hadarin rubewa saboda haramcin da gwamnatin sahyoniyawan ta […]

Afrika ta Kudu ta karyata ikirarin Trump na kisan kiyashin fararen fata

Afrika ta kudu ta karyata ikirarin da shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kan cewa kasar ta aikata kisan kiyashi kan manoma fafaren fata a Afrika ta Kudun. Ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu, Senzo Mchunu, ya yi fatali da ikirarin naTrump, yana mai cewa bai da tushe balle makama, in ji jaridar Daily […]

Karon farko an tattauna kai tsaye tsakanin ECOWAS da AES

A karon farko an fara tattaunawa tsakanin kungiyar ECOWAS da ta AES ta kawancen kasashen nan guda uku na Sahel da suka balle. Shugaban hukumar ECOWAS, dan kasar Gambia Omar Touray, ya tattauna a birnin Bamako da ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar AES wato Mali, Burkina da kuma Nijar. Wannan dai shi ne […]

SojojinHKI Sun Kashe Akalla Mutane 75 A Gaza A Ranar Jumma’a Kadai

Sojojin HKI sun sabonta hare-hare a ranar Jumma’a kan fararen hula a kan Falasdinawa a Gaza, inda suka kashe akalla mutane 76 ajiya jumma’a kadai sannan wasu dadama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa sojojin HKI sun kai hare-hare a kan wani gida […]

Donal Trump Ya Kori Gomomi Daga Cikin Ma’aikata A Majalisar Tsaro Ta Kasar Amurka

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sallami ma’aikata da dama a majalisar tsaron kasar Amuka saboda gazawarsu wajen magance wasu al-amuran tsaro da siyasa a kasar. Tashar talabijin Ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Rauters yana cewa ma’aikatan maimakon su magance al-amuran tsaro da suka shafi tsaron kasa, sai sun zauna […]

Jonh Kerry Ya Ce HKI Ba Zata Iya Wargaza Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran ba

Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka JohnKerry ya bayyana cewa HKI bata isa ta wargaza cibiyoyin makamacin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dilancin labaran IP na klasar  Iran ya nakalto Kerry na fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa babban al-amari a cikin duk wani kokari na kauda cibiyoyin Nukliyar kasar Iran […]

A Yemen An Yi Gangamin Miliyoyin Mutane Na Nuna Goyon Bayan Falasdinawa

A jiya Juma’a miliyoyin mutane Yemen sun cika dandalin ” Saba’in” dake birnin Sanaa, domin nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu. An bai wa gangamin taken: ” Muna tare da Gaza” domin jaddada ci gaba da nuna goyon bayan  al’ummar Falasdinu da suke fuskantan kisan kiyashi daga sojojin HKI, da kuma nuna kin amincewa […]

Arakci Ya Jaddada Muhimmanci Kawo Karshen Yakin Gaza Da Kuma Shigar Da Kayan Agaji

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Arakci  wanda ya gana da takwransa na fadar Vatican ya yi kira da a kawo karshen  laifukan  da ‘yan mamaya suke tafkawa akan Gaza da gaggawa a kuma shigar da kayan agaji zuwa yankin. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya je kasar Italiya domin tattaunawar bayan […]