Ana Kara Samun Karuwar Sojojin HKI Da Suke Kashe Kansu

Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato tashar talabijin din ‘aljazira’ tana fadin cewa: ” yawan sojojin da suke kashe kansu, da kuma

Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato tashar talabijin din ‘aljazira’ tana fadin cewa: ” yawan sojojin da suke kashe kansu, da kuma masu kamuwa da cutukan kwakwalwa yana karuwa.”

Majiyar tsaron ‘yan sahayoniya ta tabbatar da cewa; sojojin nasu sun shiga wannan halin ne na kashe kai da tabin kwakwalwa, tun bayan da su ka shiga Gaza.

Tun da yakin Gaza ya barke, an sami sojojin 9000 da su ka sami tabin kwakwalwa, kuma a halin yanzu suna karbar magunguna daga asibitocin mahaukata.

Su kuwa sojojin da suke kashe kansu, ba a yi musu jana’izar soja don haka ba a bayyana adadinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments