A jiya Lahadi ne da misalin karfe 6:00 na marece aka rufe akwatinan zaben, bayan da al’ummar su ka wuni suna kada kuri’un zaben ‘yan majalisar dokoki wanda shi ne karo na farko a cikin shekaru 13.
Ana san ran cewa a ranar 15 ga watan Janairu sakamakon farko zai fito, sai kuma ranar 31 ga watan janairu a sanar da sakamako na karshe.
Sai dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar ta kauracewa zaben ‘yan majalisar bayan da ta zargi mahukuntan kasar da cewa ba su bi ka’idojin zabe mai inganci ba.
Kasar Chadi tana da mutanen da su ka kai miliyan 18, tana fuskantar rashin yin zabukan da babu kwana-kwana a ciki, tun da sami ‘yanci daga Faransa a 1960.
Da akwai mutane miliyan 8 da su ka yi rijistar yin zaben ‘yan majalisa 188 a sabuwar majalisar kasar.
Zaben na jiya Lahadi dai ya zo ne a daidai lokacin da kasar take cikin yanayi mai wuya da ya hada da na tsaro, da ya hada da kungiyar Boko Haram.