Iyalan Fursunonin ‘Yan sahayoniya da suke a hannun ‘yan gwgawarmaya a Gaza, sun gudanar da Zanga-zanga a birnin Tel Aviv ta yin kira ga Netenyahu da gwamnatinsa da su amince da sharuddan Hamas na musayar fursunonin.
Wannan dai ba shi ne karon farko da iyalan fursunonin suke yi wa Netenyahu da gwamnatinsa Zanga-zanga ba, saboda su amince akan sharuddan da kungiyar Hamas da gindaya na ganin an sako musu ‘yan’uwa.
Iyalan fursunonin sun yi gangami a bakin ginin majalisar Knesset, suna yin kira ga Netenyahu da ya yi murabus, saboda samun damar dawo da dangin nasu.
Bayan shan kashi mafi girma da HKI ta yi a sanadiyyar farmakin “Guguwar Aqsa a ranar 7 ga watan Oktoba, a halin yanzu suna fuskantar rikicin cikin gida mai girma daga iyalan fursunonin da suke hannun ‘yan gwgawarmaya.
Jagoran adawa da gwamnatin Netenyahu Yair Lapid wanda ya halarci wurin Zanga-zanga ya fadawa wadanda su ka taru cewa; Gudanar da zabuka cikin gaggawa ba zai jefa Isra’ila cikin matsalar da tafi wacce take a ciki a yalin yanzu ba.