Dubun dubatar mutane ne da su ka fito daga yankunan Iran mabanbanta ne su ka cika a garin Karman domin sake jaddada alkawali da riko da tafarkin shahada a gaban hubbaren shahid Kassim Sulaimani.
Kwanaki biyu a jere kenan da gundumar ta Karman take karbar baki daga sassan Iran mabanbanta, idan wasu su ka yo tattaki daga wuraren masu nisa, domin isa hubbaren na Shahid Kassim Sulaimani.
Masu ziyarar dai sun hada maza da mata da kuma kananan yara, da suke nuna kaunarsu ga Shahid Sulaimani wanda ya sadaukar da kai domin ganin zaman lafiya ya samu a yammacin Asiya.
A wannan shekarar kamar sauran shekarun da su ka gabata an kafa hemomi a tsawon hanyoyin da suke zuwa garin na Kerman domin gabatar da hidima ga mutane da su ka hada abinci da shayi da kuma lemu.
A jiya Laraba jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya gabatar da jawabi akan zagayowar lokacin shahadar Shahid Kassim Sulaimani wanda ya kasance gwarzon kafa fagagen daga na gwagwarmaya.
Bugu da kari jagoran ya yi Magana akan halin da Syria take ciki sannan ya ce: Tabbas samarin kasar Syria za su take sansanonin Amurka da kafafunsu, kuma za su sami nasara da murkushe wadanda su ka mamaye kasarsu, ko badade ko bajima.
Jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Duk wata kasa wacce ta janye sanadarorinta na karfi da take da su, to abinda ya faru da Syria na mamayar Amruka da HKI da wasu kasashen yanki, zai iya faruwa da ita.”