A wani gagarumin farmaki da aka kai kan cibiyar leken asirin yahudawan sahayoniyya a cikin kasar Iran, an kama wani mutum tare da yi masa shari’a bisa zargin hadin kai da hukumar leken asirin ‘yan sahayoniyya, bisa tuhumarsa a matsayin maci amana da gudanar da barna a kan doron kasa. An zartar da hukuncin ne bayan kammala shari’ar laifuka da kuma tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke.
A cikin wani hadadden aikin fasaha da leken asiri a cikin kasar, an kama Isma’il Fakri a watan Disamban shekara ta 2023 yayin da yake da alaka da hukumar leken asiri da ta’addanci na ‘yan sahayoniyya.
A cikin takardun shari’ar, Isma’il Fakri, a yayin da yake yin aiki da hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya ta Mossad, ya yi yunkurin mika bayanan sirri na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga makiya domin samun kudade.
A yayin hadin gwiwarsa da hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya Isma’il Fakri ya tattauna da jami’an hukumar Mossad guda biyu.