An Zargi Kasar Faransa Da Hannu A Kokarin Juyin Mulki A Kasar Chadi

Masana sun bayyana cewa: Kasar Faransa tana da hannu a shirya  makarkashiyar kifar da gwamnatin Chadi Hari da makami da aka kai kan fadar shugaban

Masana sun bayyana cewa: Kasar Faransa tana da hannu a shirya  makarkashiyar kifar da gwamnatin Chadi

Hari da makami da aka kai kan fadar shugaban kasar Chadi da yammacin Larabar da ta gabata, gwamnatin kasar ta bayyana cewa: harin ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda 18 tare da raunata wasu 6 na daban da ake tsare da su a gidan yari, baya ga kashe wani soja, kuma farmakin ya janyo ayar tambaya kan manufar harin, da wadanda suke bayan harin, lamarin da ya janyo cece-ku ce a cikin kasar da wajenta.

Harin dai ya zo ne kasa da sa’o’i 48 bayan wani kazamin fada tsakanin kasashen Chadi da wani gungun sojojin masu goyon bayan kasar Faransa, biyo bayan sukar da Macron ya yi a birnin Paris kan shugabannin kasashen Afirka da dama, kamar yadda masu lura da al’amura ke cewa: Kasashen da Faransa ta yi musu mulkin mallaka kuma tana ganin ya zame hakki a kansu su yi mata godiya tare da sakar mata mara ta kwashe arzikin kasashensu a ganinta amma ba su yi hakan ba lamarin da ya Sanya take kunna makarkashiya kansu.

Kamar yadda Macron ya tunatar da cewa: “Babu daya daga cikin wadannan kasashe da za ta samu ‘yancin kai in ba tare da tsoma bakin Faransa ba don tallafa musu wajen samun ‘yancin kai, kuma babu daya daga cikinsu da zata iya tafiyar da kasarta mai cin gashin kanta ba tare da tsoma baki ba Faransa ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments