Masu bakin fada a ji a kasar daga kan shugaban kasa sun halarci jana’izar ta tsohon shugaban kasar da aka yi a mahaifarsa ta Daura dake arewa maso yammacin kasar.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura tawagar manya-manyan Jami’an gwamnati 25 zuwa jihar Katsina don halattar Jana’izan da za’a yiwa tsohon shugaba marigayi Muhammadu Buhari jana’iza.
Jaridar Premium times ta sami sanarwa wacce ministan yada labarai Mohammed Idris ya sanyawa hannu yana cewa tawagar za ta ci gaba da zama a Daura na jihar katsina har zuwa kwanaki uku da za’a ya masa addu’a ta karshe.
Buhari ya zama shugaban kasar Najeriya har sau biyu, daga watan jenerun shekara 2015-2023, sannan kafin haka ya rike kasar daga 1984-1985 a matsayin soja.
A makon da ya gabata ne ya je birnin Londan na kasar Burtania amma sai rai yi halinsa a ranar Lahadi.