Cibiyar dake kula da ilimin kasa ta kasar Jamus ( GFZ) ta sanar da cewa, girgizar kasar da ta faru a Turkiya ta kai daraja 6.1 a ma’aunin motsin karkashin kasa.
Girgizar dai ta faru ne da misalin 10;48 na daren jiya a nisan kilo mita 10 karkashin kasa.
An yi karar girgizar kasar a birnin Istanbul da sauran garuruwan da suke zagaye da shi.
Ya zuwa yanzu dai babu wani rahoto akan asarar rayuka da girman asarar dukiyar da ta haddasa.