Search
Close this search box.

An Tabbatar Da Ingancin Zaben Shugaba Madoro Na Kasar Venezuela

Hukumar zaben kasar Venezuela ta fidda sabon sakamakon zaben shugaban kasar inda ta tabbatar da ingancin zaben shugaba Madoro a matsayin shugaban kasar tare da

Hukumar zaben kasar Venezuela ta fidda sabon sakamakon zaben shugaban kasar inda ta tabbatar da ingancin zaben shugaba Madoro a matsayin shugaban kasar tare da samun kashi 52% na yawan kuri’un da aka kada.

 Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar zaben kasar Alus Omurusu yana fadar haka, ya kuma kara da cewa a sake irga kashi 97 % na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa a ranar Lahadin da ta gabata, kuma sakamakon ya nuna cewa dan takarar jam’iyyun adawa Admuwandu Gwanzalis ya sami kashi 43 % na kuri’un, a yayinda shugaban Madoro ya tashi da kashi 52 % daga cikin kuri’un da aka kada.

Hukumar zaben ta sake bada sakamakon wannan zaben ne a dai dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka ta ki amincewa da sakamakon zaben, sannan ta ce dan takarar yan adawa Admuwandu Gwanzalis ne ya lashe zaben.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce shugaban yan adawa ne ya lashe zaben shugaban kasa a kasar Venezuela, kuma dole ne Madoro ya mika masa shugabancin kasar. Ya ce Madora ya yi magudi ne a zaben da ya bashi nasara.

Kafin haka dai kasashen da suke makobtaka da kasar ta Venezuela wadanda suka hada da Agentina, Costorica, Ekwado, Gwatamala, Panama, Paraguwah, Peru, Jumhuriya Deminica, da kuma Uragua sun fidda jawabin hadin giwa inda suka bukaci a sake irga kuri’un zaben shugaban kasa a gaban idan masu Sanya ido daga kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments