An Sami Bullar Cutar Ebola A Karo Na Uku A Kasar Kenya

Mahukuntan kiwon lafiya na kasar Kenya sun sanar da bullar cutar Ebola a tare da wata mace 'yar shekaru 65, wacce kuma tana da alaka
kokarin hana yaduwar Ebola

Mahukuntan  kiwon lafiya na kasar Kenya sun sanar da bullar cutar Ebola a tare da wata mace ‘yar shekaru 65, wacce kuma tana da alaka da mutane biyu na farko da aka sami cutar a tare da su.

Matar dai an killace ta tun a ranar 6 ga watan Oktoba, kuma an riga ganin bullar alamomin wannan cutar a tare da ita da su ka hada zazzabi, da bushewar makogwaro da kuma mutuwar jiki.

A makon da ya wuce ne dai aka fara sanar da bullar cutar ta Ebola a kasar ta Kenya a tare da wani dan kasuwa mai shekaru 40 wanda kuma ya rasu a ranar 5 ga watan Oktoba,bayan da dawo daga kasar DRC.

Mutum na biyu da ya dauki cutar dan’uwan na farko ne,kamar yadda sanarwar ma’aikatar lafiya ta sanar.

Mahukuntan sun ci gaba da cewa; A tsakanin mutane 130 da cutar ta kama, an killace mutane 127 daga cikinsu.

A can kasar DRC dake a matsayin cibiyar bullar wannan cuta, an sanar da cewa ta shafi fiye da mutane 9,000 ta kuma dauki rayukan mutane 4,300.

Wasu kasashen makwabta da cutar ta shiga sun hada da Uganda da kuma Rwanda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted