An Sake Zaben Lula, A Matsayin Shugaban Brazil

Lula da Silva, ya lashe zaben ne da kusan kashi 51.8% na kuri'un da aka kada.

Luiz Inácio Lula da Silva ya sake zama shugaban Brazil na tsawon shekaru hudu masu zuwa, Bayan kada abokin hamayyarsa, Flavio Bolsonaro a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na ranar Lahadi.

Lula da Silva, ya lashe zaben ne da kusan kashi 51.8% na kuri’un da aka kada yayin da abokin karawarsa dan tsohon shugaban kasa Jair Bolsonaro ya samu kashi 48.2% duk da goyon bayan shugaban Amurka Donald Trump.

Wannan sakamakon a cewar masana ya bayar da shaida bayyananniya kan jajircewar al’ummar Brazil wajen kare dimokuradiyya, ci gaban al’umma, da kuma ikon mallakar kasa.

Shugaba Lula ya bayyana a ranar Lahadi, bayan sake zabensa, cewa ‘yan Brazil “sun je kaɗa ƙuri’a ne saboda mun yi nasarar shawo kansu cewa kaɗa ƙuri’a yana da mahimmanci wajen tabbatar da dimokuraɗiyya.”

Wannan shi ne karo na farko tun bayan da Brazil ta koma tsarin zaɓen shugaban ƙasa kai tsaye a shekarar 1989, da ɗan takarar da ya zo na biyu a zagayen farko ya yi nasarar lashe zabe a zagayen karshe.  

Dan takarar jam’iyyar Conservative Flavio Bolsonaro ya bayyana a ranar Lahadi cewa zai yi kira da a “soke zaɓen”

A zagayen farko a ranar 4 ga Oktoba, Flávio Bolsonaro ne ya kasance kan gaba da kashi 47.03, yayin da Lula ya samu kashi 45.16.

Tuni zababen shugaban ya fara samun sakonnin taya murna, inda Shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum ta bayyana cewa: “Ranar dimokuradiyya, mutanen Brazil sun yi nasara. Ina taya shugaba Lula murna.”

Haka zalika Shugabanni daga kasahen Paraguay, Uruguay, Bolivia, Panama, da Cuba su ma sun ba da sanarwar taya murna, tare da jaddada ci gaba da rawar da Brazil ke takawa a matsayin ginshikin ikon mallakar yankin Latin Amurka da hadin gwiwar Kudancin Duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted