An Rufe Cibiyar Musulunci ta “Humburg” Dake Kasar Jamus

Jami’an tsaron kasar Jamsu sun kai hari a jiya Laraba akan cibiyar musulunci ta “Humburg’ inda su ka sanar da killace tad a kuma dukkanin

Jami’an tsaron kasar Jamsu sun kai hari a jiya Laraba akan cibiyar musulunci ta “Humburg’ inda su ka sanar da killace tad a kuma dukkanin sauran cibiyoyin da suke a karkashinta bisa zargin cewa suna sukar HKI.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Jamus, ta bakin ministarta Nancy Firer, ta sanar da cewa, ba  su laminta da duk wata suka da za a yi wa Isra’ila ba.

Bugu da kari, jami’an ‘yan sandan kasar ta Jamus sun kai wasu jerin hare-haren akan wasu cibiyoyin musulunci har guda 54 a cikin  jahohi 7.

Ministar dai ta bayyana haka ne ba tare da ambaci ta’asar da HKi take tafkawa ba akan al’ummar Falasdinu da yi musu kisan kiyashi.

Saboda akwai kungiyoyin da suke goyon bayan HKI A Jamus, duk suna akan ta’asar da HKI take yi a Falasdinu ana daukar shi a matsayin kin jinin yahudawa.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da jami;an tsaron kasar ta Jamus suke kai wa cibiyoyin musulunci hari a kasar, bisa dalilai masu alaka da sukar siyasar HKI akan al’ummar Falasdinu.

An kafa cibiyar musulunci ta Humburge ne tun a  1953 a karkashin babban marja’in shi’a na wancan lokacin, Ayatullah Burujardi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments