An Rantsar Da Trump A Matsayin Shugaban Amurka Na 47

An rantsar da Donald Trump a wannan Litinin, inda zai jagoranci Amurka a wani wa’adin mulki karo na biyu. Trump zai gaji kujerar shugabancin Amurka

An rantsar da Donald Trump a wannan Litinin, inda zai jagoranci Amurka a wani wa’adin mulki karo na biyu.

Trump zai gaji kujerar shugabancin Amurka ne daga hannun Joe Biden, bayan da ya kada abokiyar hamayarsa ta jam’iyyar Democrat Kamala Hariss a zaben da ya gabata.

Donald Trump ya zama shugaban kasar Amurka na 47 a hukumance, bayan bikin rantsar da shi da aka gudanar a cikin babban dakin taro na birnin Washington.

Bayan an rantsar da shi, ana sa ran zai rattaba hannu kan wasu dokoki da suka hada da na shige da fice, makamashi da kasuwanci.

Trump mai shekaru 78, zai kasance shugaban Amurka mafi tsufa da aka taba rantsar da shi, bayan wa’adinsa na farko a Fadar White House tsakanin 2017 da 2021.

Zababben shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa zai soke jerin umarnin da gwamnatin Biden ta zartas sa’o’i kalilan bayan an rantsar da shi a yau Litinin.

Donald Trump ya bayyana haka ne jiya Lahadi, inda ya ce cikin umarnin da zai rattabawa hannu akwai wanda ya shafi tsaron iyakokin kasar, da na makamashi, da kudin da gwamnatin tarayya ke kashewa, da dandalin TikTok da sauransu.

A cewar wani jami’in fadar White House Trump zai kuma yin afuwa ga mutanen da aka samu da laifin harin da aka kai majalisar dokoki a ranar 6 ga Janairu, 2021.

Shugaba mai barin gado Joe Biden ya halarci bikin, sabanin Trump wanda ya kauce masa shekaru hudu da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments