An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau

An rantsar da Gen Horta N’tam a matsayin sabon shugaban mulkin sojan kasar Gunea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. Gen Horta N’Tam ya

An rantsar da Gen Horta N’tam a matsayin sabon shugaban mulkin sojan kasar Gunea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Gen Horta N’Tam ya zamo shugaban da zai mika mulki ga shugabannin farar hula inda zai kasance a kargar mulki na tsawon shekara guda.

An dai rantsar da shugaban ne a wani takaitacce kuma gajeren bikin da aka yi ranar Alhamis.

Wasu kungiyoyin farar hula a Guinea-Bissau sun soki shugaban da aka hambare, Umaro Sissoco Embalo da kitsa juyin mulki na wasan kwaikwayo a kansa,  bisa taimakon sojoji, inda suke cewa ya shirya wasan kwaikwayon ne domin hana sakamakon zaben da aka yi ranar Lahadi fitowa idan bai yi nasara ba.

Sun ce sun kwace ikon ne domin dakile wani yunkurin ƴan siyasar kasar wadanda “ke tallafa wa wani gungu da ke ta’ammali da kwaya” sannan sojojin sun kuma rufe iyakokin Kasar tare da sanya dokar hana zirga-zirga da daddare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments