Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Habasha sun rattaba hannu ne akan yarjejeniyar aikin soja a tsakaninsa a wurin baje kolin jiragen sama na wannan shekara ta 2025 a birnin Dubai.
A bangaren Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda ya wakilce ta shi ne Janar Ibrahim Nasir al-Alawi, wanda wakilin ma’aikatar tsaro ne, sai kuma janar Rashid Muhammad al-Shamsi da shi ne kwamandan rundunar sojan sama.
A bangaren kasar Habasha kuwa wanda ya wakilce ta kuwa shi ne kwamandan rundunar sojan Saman kasar Laftanar janar Yilma Midasa Janaba.
Kasashen biyu dai suna da alaka a fagen aikin soja, da a shekarar 2019 ne su ka fara rattaba hannu akan yarjejeniyar aikin tare a wannan fagen.
A shekarar 2023 ma dai kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar fahimta juna da aiki tare a birnin Addis Ababa. Fagagen da wannan yarjejeniyar ta kunsa sun hada tattalin arziki, kai da komowar kudade, zuba hannun jari da kuma fada da ayyukan ta’addanci.