Sojojin HKI sun sanar da cewa an kashe biyu daga cikinsu a yakin da yake gudana a yankin Gaza
A yau Talata ne dai sojojin mamayar su ka sanar da cewa, biyu daga cikin jami’ansu na soja sun halaka a fadan da ake yi a Gaza, daya daga cikinsu mai suna Itan Yisra’il Shiknai dan shekaru 24, wanda mataimakin kwamandan bataliya ta 932 ne. Shi kuwa na biyun day a halaka sunashi Dapir Tision Rifah dan shakaru 28, kwamanda ne na rundunar Nahal.
Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da yakin na Gaza yake cika shekaru 459, kuma sojojin mamaya suke cigaba da kai hare-hare akan Falasdinawa.
A jiya Litinin kadai Falasdinawa 22 ne su ka yi shahada,yayinda ake cigaba da fada a tsakanin ‘yan mamaya da ‘yan gwgawarmaya a Gaza.
A can yammacin kogin Jordan ma Falasdinawa guda biyu sun yi shahada sanadiyyar harbinsu da sojojin mamaya su ka yi a garuruwan Nablus da Tubas.