Search
Close this search box.

Sojojin Isra’ila 10 Aka Kashe A Zirin Gaza Ranar Asabar

Isra’ila ta ce an kashe mata sojoji takwas, a lokacin wani samame a birnin Rafah da ke Kudancin Gaza. Rundunar sojin Isra’ilan ta ce dakarun

Isra’ila ta ce an kashe mata sojoji takwas, a lokacin wani samame a birnin Rafah da ke Kudancin Gaza.

Rundunar sojin Isra’ilan ta ce dakarun suna tafiya ne a cikin motar sulke a lokacin da wani bom ya tashi da su.

To saidai kungiyar Hamas ta ce ta harba wata roka a kan motocin yakin Isra’ila, kuma sun yi ikirarin nasarar harin.

Rundunar ta kuma ce an kashe wasu sojoji biyu a arewacin Gaza a ranar ta Asabar a lokacin da wani bam ya tashi a kan tankarsu.

Wannan ya sanya adadin sojojin na Isra’ila da aka Kashe ranar Asabar, ya kasance mafi muni tun watan Janairu a yankin.

Adadin sojojin Isra’ila da aka kashe tun bayan mamayar Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba zuwa akalla 307, a alkalumman da shafin yanar gizon sojojin na Isra’ila ya fitar.

A wani labarin kuma  Isra’ila ta sanar da abin da ta kira dakatar da aikin soji na kowacce rana a wasu yankunan arewacin Gaza.

A wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila ta fitar, ta ce sojoji za su tsagaita ayyukansu tsakanin karfe 8 na kowacce safiya zuwa 7 na dare, a hanyoyin da suka dangana da Kerem Shalom zuwa titin Salah al-Din.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments