An Kashe Mutane Fiye Da 40 A Rikicin Siyasa A Afirka Ta Kudu

Mafi yawancin wadanda aka kashe shi din 'yan siyasa ne da kuma kungiyoyin fararen hula da kuma sarakunan gargajiya.
shugaba Remaphosa

A daidai lokacin da kasar ta Afirka take fuskantar zabukan kananan hukumomi nan da wata daya,yawan mutanen da aka yi wa kisan gilla masu alaka da siyasa, sun kai 43.

A ranar 4 ga watan Nuwamba ne za a yi zabukan kananan hukumomi, da jam’iyyun adawar kasar suke son samin nasara akan jam’iyyar ANC mai Mulki bayan koma bayan da aka samu a kasar a fagen tsaro da kuma karuwar cin hanci da rashawa.

Wata cibiya mai fada da tsararrun laifuka ( GI-TOC) ta sanar da cewa daga farkon wannan shekara zuwa30 ga watan Satumba, wadanda aka yi wa kisan gilla da ake ta’allaka shi da siyasa sun kai 45.

Mafi yawancin wadanda aka kashe shi din ‘yan siyasa ne da kuma kungiyoyin fararen hula da kuma sarakunan gargajiya.

A makon da ya wuce ma dai a kasar ta Afirka ta kudu an fitar da wasu alkalumma da suke nuni da cewa an kashe mata 10 a lokuta daban-daban, ba tare da an iya gano cikakkiyar alakar da take a tsakaninsu ba ko dalilin yin hakan.

Kasar Afirka Ta Kudu tana cikin kasashen duniya da aka yi yin kisan gilla.

Sojojin Kasar Yamen Suna Samun Nasara A Gundumar Ta’iz Rahotanni daga birnin San’aa na kasar Yemen suna cewa, sojojin kasar suna ci gaba da samun nasara a fafatawar da suke yi da mayakan da suke samun goyon bayan Saudiyya da kuma sojojin na Saudiyya a gundumar Ta’iz.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted