Majiyar kiwon lafiya a kasar Sudan ta bada sanarwan cewa a cikin mako guda kacal an kashe mutane 114 a yakin da sojojin kasar da kuma yan tawaye na RSF suke fafatawa.
Shafin yanar gizo na labarai ARAB NEWS na kasar Saudiya ya bayyana cewa, jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kai hare-hare kan garin El-Obeid babban birnin Lardin Kordufan na raewa inda suka lalata injunan bada wutan lantarki na garin sun kuma jawo mutuwar mutane da dama.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya kara da cewa a halin yanzu sojojin kasar sun kori dakarun RSF zuwa kusa da kan iyaka da kasar Chadi da kuma lardin Kordofan. Banda haka an kashe mutane 51 a fafatawar Ranar Lahadin da ta gabata a yankin Darfor.
Labarin ya kara da cewa a halin yanzu bangarorin biyu suna fafatawa ne a tsakanin Garin Al-Fashir wanda ke karkashin ikon dakarun yan tawaye na RSF da kuma Al-Zuruq wanda yake da tazarar kilomita 180 kacal daga Al-Fashir cibiyar sojojin RSF.
Labarin yace hare-haren RSF kan sun kashe fararen hula da dama, sannan bangarorin biyu suna zargin juna da kashe fararen hula. Zuwa ranar Jumma’a da ta gabata an kashe mutane 63 a kan iyaka da kasar Chadi a kusa da garin Kernoi.