Wani bayuhude dan share wuri zauna ya halaka a yayinda wasu 30 sun ji rauni a lokacinda wani makami mai linzami samfurin Bilistic daga kasar Yemen ta fada kan birnin Telaviv babban birnin HKI.
Sannan yahudawan sun kai wasu sabbin hare-hare a kan kasar ta Yemen a jiya da dare.
Jaridar ‘Arutz Sheva’ ta HKI ta bada labarin cewa makamin ya fada kan wani wuri mai tazarar kilomita 5 kacal dafa babban birnin kasar Tel’aviv. Har’ila yau wani bayahude mai su na Benyamin Bleacher dan shekara 68 ne ya halaka sanadiyyar jiniyoyin da suka tashi don gargadi daga faduwar makamin.
Sannan tashar radiyo ta ‘Kan Broadcaster’ ta yahudawan ta ce wasu yahudawa 30 ne suka ji rauni sanadiyyar farduwar makamin a garin Jaffa kusa da Tel’aviv babban birnin kasar. Labarin ya kara da cewa wannan shine hari na ukku a cikin kwanaki biyu da suka gabata.
Sojojin Yemen dai suna kaiwa HKI hare-hare da makamai ma su linzami irin wannan tun ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023. Don taimakawa Gaza, Wanda ya zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa 45,200