Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Iran ta fitar da sanarwa da take karyata cewa,an rufe filayen jiragen saman kasar, tare da tabbatarwa da matafiya su rika tuntubar hanyoyin da su ka dace domin samun bayanai masu inganci.
Hukumar ta kuma ce; Abin takaici ne yadda wasu kafafe suke watsa kirkirarrun labarai dangane da zirga-zirgar jiragen sama tare da riya cewa, an sami matsala a cikin hanyoyin sadarwa na filin saukar jiragen sama, ba domin komai ba, sai saboda su rikita matafiya.
Hukumar ta ce ita kadai ce take da hakkin fitar da bayanai akan zirga-zirgar jiragen sama, ko kuma wasu sauye-sauye da za su iya faruwa a cikinsu.