Iran ta ce ta samu nasarar karbar siginar na farko daga taurarin dan adam guda uku da ta harba zuwa sararin samaniya a jiya.
Ministan Sadarwa da Fasaha na Iran ya sanar da cewa an samu nasarar karbar siginar farko daga taurarin dan adam na kasar guda uku, Zafar 2, Paya, da Kosar, wadanda aka harba zuwa sararin samaniya a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa wannan yana tabbatar da ingancin fasaha da kuma yadda taurarin dan adam din ke aiki bayan an sanya su a sararin samaniya.
Seyyed Sattar Hashemi ya jaddada a daren Lahadi cewa karbar siginar shi ne babban mataki na farko bayan kaddamar da tauraron dan adam din.
Ya kara da cewa wannan nasarar tana ba da damar ci gaba da sa ido kan fasaha da kuma fara matakai na gaba na ayyukan da aka tsara.
A jiya Lahadi ne Iran ta harba taurarin dana dam guda uku akan rokar cilla tauraran dan adam ta Soyuz ta Rasha.