An Kammala Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Ghana

A Ghana yau ake sa ran rufe gangamin yakin neman zabe a babban zaben kasar Ghana. Mutum 12 ne ke takarar neman kujerar shugabancin kasar

A Ghana yau ake sa ran rufe gangamin yakin neman zabe a babban zaben kasar Ghana.

Mutum 12 ne ke takarar neman kujerar shugabancin kasar domin maye gurbin Shugaba Nana Akuffo Addo, wanda ke kammala wa’adinsa na biyu.

Sai dai an fi ganin fafatawar za ta fi zafi tsakanin Mataimakin Shugaban Kasa Mahamudu Bawumia na jam’iyyar NPP, da tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama a karkashin jam’iyyar hamayya ta NDC.

Za a kada kuri’a a zaben shugaban kasar ta Ghana a ranar Asabar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments