An Kammala Gasar ‘Rayan’ Na AI Ta Kasa Da Kasa A Nan Tehran

An kammala gasar gina manhajan komfuta ta kasa da kasa farko a jami’ar Amir Kabir take nan Tehran . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar

An kammala gasar gina manhajan komfuta ta kasa da kasa farko a jami’ar Amir Kabir take nan Tehran .

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an gudanar da gasar ne  tsakanin kasashe 30 daga yankuna daban daban na duniya, kuma an kammala gasar a jiya Jumma’a 28 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Gasar Rayan dai ita ce gasa na manhajan AI ko kirkirarren fasaha mafi girma a duniya. Gasa wanda yake samar da mahaja ya kula da ita tare da amfani da fasahar AI.

Gasar sharar fage ta Rayan wanda aka gudanar a dukkan jihohon Iran ya sami halattar mutane 30,000 daga kasashe 137 a duniya. Amma a gasa ta karshe da aka kammala mutane kimani 100 ne daga kasashen 30 suka sami halattar gasar.

Kasashen da suka halarci gasar sun hana da Amurka, Russia, China, India, Italy, Argentina, Chile, Poland, Romania, Singapore, Vietnam, Colombia, Armenia, Pakistan, Bangladesh, Afghanistan, Australia, Belarus, Serbia, Ethiopia, Ukraine, Taiwan, Kazakhstan, Slovakia, da kuma Iran.

Ministan fasaha da technoloji Hussain Afsheen yace Raya ta fi karfin gasa, sai dai shiri ne na adana fahinta da fasaha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments