Jami’an tsaro a kasashen turai kimani 25 ne suka kama daliban makarantu masu yawa, wadanda suke zanga zangar nuna rashin amincewarsu da yakin da kasashen suke shiga ko suke kokarin shiga.
Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya bayyana cewa, a jiya Jumma’a 20 ga watan Nuwamba ne aka gudanar da zanga zanga a kasashen turai 25 cikin 27 , a wani gagarumin zanga zanga na nuna rashin amincewa da yake yaken da kasashen suke fafatawa da kuma mai yuwa zasu shiga nan gaba.
Dubban daruruwan dalibai da malamansu da shiekhunan malaman jami’o’ii ne suka fito tattakin wanda aka gudanar a garuruwa ko wurare 400 a kasar Ingila kadai. .
Daliban da malamansu suna rare taken “Munason a kola da abinda yake gabammu, ba yake yakensu ba”. Sun yi kira ga gwamnatocin kasashen Turai su kawo karshen yakin da Amurka ta fara a Iran, saboda shi ne ya sasu cikin kunshin rayuwa, sanadiyyar karancin makamashi da bukatun rayuwa.
Har’ila yau daliban da kuma wasu masu ragin kare al-ummar Falasdinu sun yi kira ga gwamnatin kasar Burtania ta kawo karshen tallafawa HKI da kudade da kuma makamai saboda tana kashe mutane wadanda basu aikata wani laifi ba.
IP yayi hira da wasu masu zanga zanga a Tranfa Square a birnin London wadanda suka bayyana cewa, suna son gwamnatin kasar Burtania ta kawo karshen goyon bayan haramtacciyar kasar Israela, wacce take kashe yara da mata a Gaza.
Wasu masu tattakin sun isa gida mai lamba 10 a titin ” Downing” na birnin London don isar da sako ga Firay ministan kasar Burtania. Amma suka hadu da wata tawaga masu goyon bayan gwamnati, sai da yansanda suka shiga tsakaninsu.