An Kai Hari da Makamai Akan Fadar Shugaban Kasar Chadi

Rahotanni da suke fitowa daga kasar Chadi sun ce mutane 19 sun rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da aka kai da makamai a fadar shugaban

Rahotanni da suke fitowa daga kasar Chadi sun ce mutane 19 sun rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da aka kai da makamai a fadar shugaban kasar a birnin N’Djamena.

Majiyar gwamnatin kasar ta ce mutane 19 ne su ka kai harin, amma tuni an kasha 18 daga cikinsu, sai kuma wani jami’intsaro daya da ya rasa ransa.

Ministan harkokin wajen kasar ta Chadi ya ce shugaban kasa yana nan lafiya lau, sojoji suna ba shi kariya.

Mazauna birnin N’Djamena sun ce sun ji kararrakin tashin abubuwa masu fashewa a zagayen fadar shugaban kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments