A wani kwarya-kwaryar biki da aka yi a nan birnin Tehran an kafe Mutum-mutumin tarihi na sarkin daular Roma Velarian wanda aka kamo shi a matsayin fursunan yaki a zamanin Daular Sasaniyawa, ya kuma durkusa a gaban sarki Shahpur 1.
Kafe Mutum-mutumin da aka yi, yana a karkashin jaddada matsayar Iran na cewa, al’ummarta ba ta rusunawa a gaban abokan gaba sai dai su rusuna a gabanta.
A shekarar miladiyya ta 260 bayan haihuwar Annabi Isa ( a.s) ne aka yi yaki a tsakanin tsohuwar daular farisa ta Sasaniyawa da kuma daukar Roma ta gabasa, a Edessa, wanda ya kare da murkushe sojojin Romawa 70,000 sannan kuma aka kama sarkinsu Velarian aka kawo shi Iran a matsayin furusunan yaki.
Har ila yau, an yaye kallabin wasu muhimman hotuna na tairhi akan yadda al’ummar Iran a tsawon tarihi su ka yi turjiya a gaban Mahara na waje da su ka hada da Alexander a shekara ta 334 gabanin haihuwar Annabi Isa ( a.s).