An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania

An sanya dokar hana fita a babban birnin Tanzaniya bayan zaben da aka yi cikin tashin hankali ‘Yan sandan Tanzaniya sun sanar da dokar hana

An sanya dokar hana fita a babban birnin Tanzaniya bayan zaben da aka yi cikin tashin hankali

‘Yan sandan Tanzaniya sun sanar da dokar hana fita da dare a birnin Darul-Salam, babban birnin tattalin arzikin kasar, a ranar Laraba da yamma bayan zanga-zangar da ta barke a daidai lokacin da ake gudanar da zaben shugaban kasa, wanda ake sa ran Shugaba Samia Suluhu Hassan za ta lashe bayan an cire babban dan takarar jam’iyyar adawa.

Kungiyar sa ido kan intanet ta NetBlocks ta ruwaito cewa: An katse ayyukan intanet a fadin kasar, yayin da bidiyo ke yawo a shafukan sada zumunta suna nuna matasa suna jifan jami’an tsaro da kuma kone-kone wasu gidajen man fetur.

Shaidun gani da ido sun kuma bayar da rahoton zanga-zangar nuna fushi a unguwanni da dama na Darul-Salaam, ciki har da kona ofishin gwamnati na yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted