Hukumar agaji ta “ Tauraruwar Dauda” ta sanar da cewa, mutane 9 ne su ka jikkata a wani hari da makami da aka kai a matsugunin ‘yan share wuri zauna na “Ar’il” dake yammacin kogin Jordan.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, 3 daga cikin wadanda su ka jikkatan suna cikin halin rai kwakwai-mutu kwakwai, yayin da ‘yan sanda su ka ce an kashe wanda ya kai harin.
Rediyon sojojin HKI ya ambaci cewa an kai harin ne akan wata motar safa a kusa da matsugunin ‘yan share wuri zauna na “ Ar’il” a yammacin kogin Jordan Jordan.
Ita kuwa jaridar “Times Ups” ta Isra’ila ta bayyana cewa, masu aikin agaji sun iya waurin da ake kira Jiti-Afisar’ wanda yake kusa da matsugunin ‘yan share wuri zauna a yammacin Kogin Jordan.
A wata sanawa da kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar dazu, ta ce wanda ya kai harin daya ne daga cikin makayanta.