Rahotanni daga yankin Falasdinu da Isra’ila ta mamaye sun tabbatar da labarin kashe wasu yahudawan Isra’ila 3 a wani farmaki da aka kai a mashigar Karama daga bangaren Falasdinu, dake daura da yankin “Allenby” daga bangaren Jordan, a kan iyakar kasar da Jordan da yammacin gabar kogin Jordan na Falastinu da ke karkashin mamayar Isra’ila.
Rahoton tashar Almayadeen ya ce, ma’aikatar lafiya ta Isra’ila ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kashe ‘yan Isra’ila uku a farmakin mashigar Karama, sannan kuma wanda ya kai farmakin direban babbar motar dakon kaya dan kasar Jordan ne, wanda shi ma sojojin Isra’ila masu gadin iyaka suka harbe shi, kamar yadda kafar yada labaran Isra’ila ta bayyana.
Gidan rediyon sojojin Isra’ila ya ce bayanan farko sun nuna cewa wani direban babbar motar dakon kaya dan kasar Jordan ya iso ne daga yankin Jordan zuwa mashigar, inda ya yi shigar da karamar bindiga cikin motar, sannan ya harbe yahudawan Isra’ila uku da ke wurin.
A nata bangaren, jaridar “Maariv” ta Isra’ila ta rawaito cewa wadanda suka mutu a harin jami’an tsaron Isra’ila ne masu alaka da ayyukan tsaroon kan iyaka, yayin da kafafen yada labaran Isra’ila suka ce sojojin Isra’ila sun kama direbobin manyan motoci a mashigar “Allenby” bayan farmakin.
Wannan farmakin na zuwa ne bayan wasu jerin hare-hare da mayakan ‘yan gwagwarmaya suka kai kan sojojin mamaya da matsugunan yahudawa a yankin yammacin kogin Jordan da kuma yankunan da Isra’ila ta mamaye a baya-bayan nan.