Amurka ta gurfanar da shugaba Nicolas Maduro na Venezuela a gabata wata kotun birnin New York kwanaki biyu bayan kame shi tare da matarra.
Hotunan talabijin daga Amurka sun nuna Nicolas Maduro, mai shekaru 63, an daure shi da sarka tare da rakiyar wasu jami’an tsaro da ke dauke da manyan makamai.
An tsara Maduro zai bayyana a gaban alkali Alvin K. Hellerstein, wani gogaggen alkali a kotun tarayya da ke Manhattan.
Rahotanni sun ce alkalin ya saba jagorantar shari’o’i masu mahimmanci masu nasaba da manyan laifuka, musamman wadanda suka shafi ta’addanci da laifukan da aka tsara.
Mista Maduro na fuskatar tuhume tuhune 25 bisa tuhumar gwamnatin tarayya da manyan tuhume-tuhume guda huɗu, wadanda suka hada da ta’addancin miyagun kwayoyi, sumogil din hodar iblis, da mallakar makaman yaki.
Tun a shekarar 2020 aka shighar da ƙarar farko kan Maduro.
Sabuwar karar ta yanzu ta kasance sabuntawa ce, tare da karin cikakkun bayanai, musamman game da matar Nicolas Maduro, Cilia Flores, wacce za ta bayyana tare da mijin nata a cewar labarin.
Za a tabbatar ko suna da lauyoyi ko kuma za a ba su daya.
Ba a bukatar Maduro da matarsa su amsa laifinsu, saidai alkalin zai iya ba da umarnin a tsare su kafin a fara shari’ar.
Shari’ar dai na iya daukar watanni da dama, ko ma fiye da shekara guda.
Ana sa ran mai kare wadanda ake zargin zai kalubalanci tuhume-tuhumen da yanayin kama su sannan a mayar da shi Amurka.