Bayan da jami’an tsaro a kasar Burtania suka kama wani fitaccen mai gwagwarmayar kare hakkin Falasdinawa da kuma goya masu baya, a kwanakin da suka gabata. Wasu yan kasar sun gudanar da taro don tattaun makomar incin fadin albarkacin baki a kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka yi magana a taron a yau Lahadi, suna cewa batun encin fadin albarkacin baki, da kuma kare hakkin b il’adama yana kara tabarbarewa a kasar.
Labarin ya kara da cewa a ranar asabar da ta gabata ce, masu zanga-zanga a manya manyan birana a kasar Burtaniya suna fito kan tituna inda suke, goyon bayan al-ummar Falasdinu, sun bukaci a kawo karshen mamayar kasar Falasdinu, a kawo karshen goyon bayan da kasashen yamma suke bawo HKI kan Falasdinawa. A kawo karshen mamayar kasashen larabawa sannan a sake gida zirin gaza bayan rusashi wanda HKI a cikin watanni 15 da suka gabata.
A birnin londan kadai, yawan masu zanga-zanga ta lumana sun kai kimani 80,000, sun bukaci a kawo karshen takurawar da suke wa kasashen Lebanon da Iran.
A yayin zanga-zangar dai yansanda sun kama mutane kimani 77 suka kuma gurfanar da su a gaban Kotu. Sanan sun bukaci fitattun yan siyasar kasar wadanda suke cikin zanga zangar wato Jeremy Corbyn tsohon shugaban jam’iyyar Labo da kuma dan majalisa John McDonnell duk su kai kansu gaban jami’an tsaro don amsa tambayoyi.