An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Kan Ci Gaba Mai Dorewa A  Ruwan Teku

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da taron kasa da kasa karo na 3 kan ci gaba mai dorewa a ruwan teku a garin Khorramshahr

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da taron kasa da kasa karo na 3 kan ci gaba mai dorewa a ruwan teku a garin Khorramshahr inda ya kunshi masu bincike da malaman jami’a da masu ruwa da tsaki kan harkokin teku domin tattaunawa kan kalubale da damammaki da ake da su na dorewar yanayi mai kyau a ruwan teku.

Taron an tsara shi ne don bunkasa tattaunawa tsakanin bangarori daban daban da kuma habaka dabarun kimiya don ci gaban teku mai dorewa, da samar da yanayi ga kwararru a Iran da ma kasashen duniya don yin bayanai kan bincike da manufofi.

haka zalika an shirya taron ne bisa turbar ci gaban harkokin kula da teku da gabar ruwa mai dorewa, taron na kwanaki biyu da aka gudanar daga ranar 27 da 28 ga watan Janeru da muke ciki ya so yayi bita kan sabbin ci gaban kimiyya da kuma kalubalen da suke fuskanta da kuma irin damarmaki da ake samu a fannoni da suka shafi bangaren teku.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted