An gudanar da gagarumar zanga-zangar kin jinin Amurka a Greenland

A Danmark an gudanar da wata gagarumar zanga zangar kin jinin Amurka game da shirinta na mamaye yankin Greenland. Masu zanga-zanga sun hau kan tituna

A Danmark an gudanar da wata gagarumar zanga zangar kin jinin Amurka game da shirinta na mamaye yankin Greenland.

Masu zanga-zanga sun hau kan tituna a Greenland da Denmark domin nuna adawa ga shirin Trump da barazanar da yake yi na kwace tsibirin.

Wata kungiya ta Greenlanders a Denmark, mai suna Uagut, ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa manufar zanga-zangar ita ce “aike da sako mai karara da hadin kai na girmama dimokuradiyya ta Greenland.”

A babban birnin Denmark na Copenhagen, mutane sun taru a gaban Babban Zauren Birnin don yin zanga-zanga zuwa Ofishin Jakadancin Amurka.

A cewar Camilla Siezing, shugabar Æ™ungiyar Inuit, masu zanga-zangar “suna bukatar girmama Daular Denmark da kuma hakkin Greenland na.”

A babban birnin Greenland, Nuuk, masu zanga-zanga sun yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Amurka dauke da tutocin Greenland don nuna rashin amincewa da “tsarin Amurka na kwace ikon Greenland.

A ranar Juma’a, shugaban Amurka ya yi barazanar sanya haraji kan kasashen da ba su bi shirinsa na kwace Greenland ba, wanda yanki ne mai cin gashin kansa da Denmark ke iko da shi.

Fadar White House ta ce a farkon wannan makon cewa Trump yana tattaunawa dabarun kwace Greenland, ta hanyar amfani da karfin soji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted