An Gudanar Da Bukukwan Ranar 30-Decemba, Ko Ranar Basira A Yau Lahadi A Nan Iran

A yau Lahadi ce aka gudanar da bukukuwan ranar ‘Basira’ wato ranar  9 ga watan Day a kalandar Iranaiywa, ranar da mutanen kasar suke ceci

A yau Lahadi ce aka gudanar da bukukuwan ranar ‘Basira’ wato ranar  9 ga watan Day a kalandar Iranaiywa, ranar da mutanen kasar suke ceci JMI daga faduwa a hannun wasu munafukai makinta wadanda suke samun goyon bayan kasashen waje a shekara ta 2009.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an gudanar da bukukuwan 9 ga watan Day ne, a duk fadin kasar don tunawa da yadda miliyoyin Iraniyawa masu kishin kasarsu da kuma addininsu suka kwarara a kan tituna a cikin birnin Tehran inda suka kawo karshen rikicin da wasu yan kasar wadanda suka saida kasarsu ga manya-manyan kasashen duniya wadanda suka dade suna jiran ranar faduwar JMI.

Wasu yan takarar shugaban kasa guda biyu ne, wadanda suka fadi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a cikin watan Yuni na shekarar suka tada fitinar.

Kuma sune, Mir Hussain Musawi da kuma Mahdi karubi, sun tada fitinar ne da sunan an yi magudi a zaben. Wanda shugaba Ahmadi Najad ya lashe.

A cikin rikicin dai an kashe jami’an tsaro na JMI da dama, sannan an lalata dukiyoyin jama’a da kuma na daddaikun mutane. Banda haka basu bare hatta masallatai da kuma Alkur’ani ba, sai da suka konasu.

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a kasar sun fidda sanarwa wacce take nuna cewa mutane masu basiri ne suka fito ranar 9 ga watan Dey shekara 1388 H.SH. a kalandar Iraniyawa,  suka kashe wutar fitinar suka kuma kubutar da JMI daga hannun kuraye wadanda suke son ganin bayan gwamnatin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments