An Gudanar Da Bikin Mauludi A Fadin Iran A Ranar Lahadi

A jiya ne aka gudanar da bukukuwan tunawa da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu da kuma Makon Hadin Kan Musulmi a birnin Tehran

A jiya ne aka gudanar da bukukuwan tunawa da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu da kuma Makon Hadin Kan Musulmi a birnin Tehran da kuma sauran fadin Iran

A daidai lokacin da Makon Hadin Kan Musulmi da kuma zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa), an gudanar da babban bikin karkashin taken “Al’ummar Ahmad” a ranar Lahadi da yamma a birnin Tehran da sauran birane daban-daban a fadin kasar, tare da halartar iyalai da sassa daban-daban na al’umma.

Bikin, wanda aka gudanar a duk fadin kasar Iran karkashin taken “Al’ummar Ahmad,” ya kunshi shirye-shirye daban-daban na al’adu, fasaha da na addini, baya ga bayar da abubuwan sha da kayan zaki ga mahalarta.

Wannan bikin mai cike da farin ciki yana jaddada wajabcin bin tafarkin Manzon Allah, Annabin Rahama Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa) da kuma karfafa hadin kan al’ummar Musulmi a dukkan fannoni na asali, mazhabobi, da kabilu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted