An Gudanar Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya Karo Na 11

an gudanar da bikicin ranar hausa ta duniya a wani karo na 11

A jiya laraba ce  aka gudanar da  bikin shekara-shekara na ranar Hausa ta Duniya da aka saba yi a duk ranar 26 ga Agusta, tun bayan assasa shi a 2015, domin tunatar da muhimmancin Harshe da kuma Al’adun Hausawa

Ranar Hausa ta Duniya dai lokaci ne na musamman da ake amfani da shi wajen tunatar da muhimmancin harshen Hausa da kuma Al’adun Hausawa, an kuma fara wannan biki ne ta kafafen sada zumunta domin daukakawa da kuma ci gaba da yada harshen Hausa a fadin Duniya.

Ranar wacce  take karo na 11 da ake gudanar da bikinta, na nufin hada kan Hausawa baya ga samar da ci gaba mai dorewa dama bunkasa harshen, wanda ke matsayin na biyu mafi girma a nahiyar Afrika.

Daga cikin batutuwan da bikin bana ya mayar da hankali kai, akwai amfani da kimiyya da fasaha wajen bunkasa Harshen Hausa da bai wa Harshen da Al’adun Hausawa kariya daga sauye-sauyen zamani daga kutsen sabbin Al’adu.

Baya ga harshen Swahili da ke da alaka da larabaci, Hausa ce kan gaba a jerin harusunan da ake amfani da su a nahiyar Afrika dama yawan jama’ar da ke amfani da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted