An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza

An sami gawar wani sojan HKI wanda ya taba yaki a Gaza wanda kuma ake zaton shi ya kashe kansa. Tashar talabijan ta Presstv a

An sami gawar wani sojan HKI wanda ya taba yaki a Gaza wanda kuma ake zaton shi ya kashe kansa.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar HKI da yaren Hebru mai suna  Yedioth Ahronoth yana fadar cewa an gano gawar sojan dan shekara 28 wanda ba’a bayyana sunansa ba a dajin dajin sweezland kusa da yankin tiberias a yau Alhamis.

Labarin ya kara da cewa, idan ya tabbata sojan ya kashe kansa ne to kuwa shi ne 17 da suka kashe kansu tun bayan fara yaki a gaza a shekara ta 2023.

Ahronoth ya cewa sojan ya yi aiki da runduna ta 99 a gaza a cikin yan makonnin da suka gabata. Sannan a halin yanzu a fara gudanar da bincike don tabbatar da abinda ya halaka shi.

Sannan idan yansanda sun kammala bincike zasu mikawa lauyoyin sojojin kasar ne don yin abinda ya  dace, musamman bayyana abinda ya kashe shi. Mutum na karshe daga sojojin HKI ta ya kashe kansa shi ne wanda yayi kwanaki 300 yana yaki bayan ya ga wani abu mai ban tsoro a yakin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments