Shuwagabannin kasashen duniya a kungiyar G20 sun gabatar da jawabin bayan taro da kuma matsayin kungiyar a cikin al-amura da dama a duniya, duk tare da kauracewa taron wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi.
Shafin yanar gizo na labarai AfricaNews ya nakalto shugaban afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yana gabatar da jawabi bayan taron shuwagabannin na G20 na kwanaki 2.
Ramanposa yace kungiyar G20 ba zata taba manta da sauyin yanayi ba, kuma ba zata kyala sauran kasashen duniyaba ba, kuma kungiyar zata yi kokarin ganin ta daga sauran kasashe raunan a duniya zuwa matsayin da ya dace na tattalin arziki.
Kakakin Ramanposa ya ce dukkan kasashen da suka halarci taron sun amince da jawabin bayan taron. Amma shugaban kasar Agentina wanda ya kauracewa taron don goyan bayan Trump ya ce bai amince da jawabin bayan taron ba.
Wannan ne karon farko wanda aka gudanar da taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya G20 a Afirka a kuma Afirka ta kudu.