Ma’aikatar makamashi ta kasar Saudia ta bada sanarwan tashin wata a babban ginin kamfanin Aramco da ke birnin Riyad, kuma hakan ya faru ne jim kadan bayan gwamnatin kasar Yemen ta yi gargadi zata yi hakan.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ma’aikatar na cewa an kai hari kan babban ginin harkokin gudanarwa na kamfanin Aramco wanda ya sa ya gama da wuta kuma ana iya ganin hayaki na tashi daga ginin.
Labarin ya kara da cewa a safiyar yau Laraba ma sojojin kasar Yemen sun cilla makamai kan ginin Aramco da ke Dahahran.
Gwamnatin ta ce ta kakkabo wasu daga cikin makaman da mayakan yemen suke ci gaba da cillawa kan kasar a yayinda ake fafatawa da sojojin kasar a cikin gudancin kasar ta Yemen wanda saudin take mamaye da shi tun shekara ta 2015.
Wasu kafafen yada labaran kasar sun bada labarin kakkabo wasu daga cikin makamai masu linzamu samfurin crusse daga kasar Yemen. Gwamnatin kasar Saudia a shekara ta 2015 ta mamaye gudancin Yemen da nufin bawa Tsohon shugaban kasar Aabdu rabbu mansur hadi damar komawa san’a a kan kujerar shugabancin kasar sannan ta dorawa gwamnatin san’a takunkuman tattalin arziki ta sama kasa da kuma ruwa, wanda a yau ya kai kimani shekaru 12. gwamnatin kasar Yemen tana bukatar dauke wadan nan takunkuman. CNN tace saudiya bata da zabi an banda tattaunawa da Yemen.