Shugaban Rasha Vladimir Putin na karbar bakuncin shugabannin kasashen Afirka 22 a Moscow a taron koli na uku na Rasha da Afirka.
Mai ba wa shugaban shawara kan harkokin diflomasiyya, Yuri Ushakov, ya fitar da ajandar taron inda ya sanar da wani shiri na tarurruka 24, ciki har da wadanda aka tsara a gefen taron kasashen da ke fitar da iskar gas a ranar 27 ga Oktoba.
An tsara yau, Vladimir Putin zai gana da shugabannin kasahen Masar, Habasha, da Jamhuriyar Congo.
Za a ci gaba da tattaunawa a gobe tare da shugabannin Burundi, Namibia, Kenya, Sudan, Madagascar, da Zimbabwe.
Washegari, ana sa ran shugaban Rasha zai gana da shugabannin Ghana, Mali, Mauritania, Sudan ta Kudu, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Togo, Eritrea, Somaliya, da Comoros.
An bayyana cewa taron zai ba da dama don duba muhimman abubuwan da suka fi muhimmanci a dangantakar bangarorin biyu da kuma gano damarmaki ga sabbin ayyukan tattalin arziki da makamashi.
A cewar Yuri Ushakov, an tsara shirin ne musamman don bai wa Vladimir Putin damar ganawa da shugabannin kowace kasa ta Afirka da aka wakilta a matakin koli.
Jimilla, kasashe 48 daga cikin 54 na Afirka sun tabbatar da halartar taron.
Vladimir Putin zai jagoranci zaman taron shugabanni tare da takwaransa na Burundi, Évariste Ndayishimiye kana kuma shugaban kungiyar Tarayyar Afirka na yanzu.
Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan noma, makamashi, zuba jari, kayayyakin more rayuwa, da fasaha.
Moscow dai na da niyyar, inganta hadin gwiwa bisa girmama juna da kuma samun damar samun albarkatu, abinci, takin zamani, da fasahohin zamani ga kasashen Afirka.