An fara taron kasa da kasa na masu gwagwarmaya musulmi daga kasashen duniya da dama a nan birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa manufar taron itace tattauna hanyoyin taimakawa masu gwagwarmayan a kasashen yakin Asiya ta kudu da kasashe masu girman kai a duniya. Da kuma Magana a kan makomar al-ummar musulmi a sabuwar duniya da ke kokarin bayyana.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daya daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a taron Qobad Mohammadi shugaban jami’ar koyon aikin likita da kiwon Lafiya a nan Tehran yana cewa: Shahidammu sun bada rayukansu ne don mu sami nasara a kan gwamnatocin mamaya a yankin Asiya ta kudu. Ya kuma kara da cewa: Duniya tana sauyawa da sauri, don haka dole ne mu fayyace matsayin musulmin a sabuwar duniyar da ke tasowa.
Mohammadi ya kara da cewa: a halin yanzu mun kai wata marhala mai muhimmanci a gwagwarmaya tsakanin gaskiya da karya. Yace: Ana yaki ne tsakanin kasashe masu girman kai a duniya da kuma masu gwagwarmaya wadanda suka bada jininsu don kare kansu daga makiya. Kuma dole ne su sami nasara a wannan gwagwarmayar.
Daga karshe muhammadi ya kammala da cewa abin bakin ciki, shi ne har yanzu wasu kasashen musulmi suna huldar kasuwanci da HKI. Wanda hakan a wannan halin da muke ciki ba taimakawa masu gwagwarmaya ba ne.