An Fara Bukukuwan Kwanaki Goma Na Cin Nasarar Juyin Juya Halin Musulinci A Iran   

Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin

Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga jirgin saman Air France da ya dawo da Imam Khumaini gida daga gudun hijira na sama da shekaru 14 wanda ya kai ga kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A yayin bukukuwan al’ummar Iran suna halartar taruka daban-daban har zuwa zagayowar ranar 22 ga watan Bahman wato 10 ga watan Fabrairu, wato ranar tunawa da juyin juya halin Musulunci.

Juyin juya halin Musulunci ba wai kawai ya sake fasalin tsarin siyasar Iran ba ne, har ma ya sake fasalin matsayinsa na duniya, tare da kafa Jamhuriyar Musulunci a matsayin sabuwar hanyar samun ‘yancin kai daga wani yanki na gabas ko na yamma.

Ta hanyar kifar da gwamnatin sarki Shah Pahlavi shekaru 46 da suka gabata, al’ummar Iran sun kawo karshen mulkin shekaru 2,500 na sarauta tare da kafa wani sabon tsarin siyasa jamhuriya mai tushe bisa kimar Musulunci da dimokuradiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments