An Fara Aiki Da Tsagaita Wutar Yaki A Gaza Cikin Dari-dari

A yau Lahadi ne aka fara aiki da tsagaita wutar yaki a tsakanin kungiyar gwagwarmayar musulunci Hamas da kuma HKI, sai dai ana ci gaba

A yau Lahadi ne aka fara aiki da tsagaita wutar yaki a tsakanin kungiyar gwagwarmayar musulunci Hamas da kuma HKI, sai dai ana ci gaba da zaman dari-dari.

 Da misalin karfe 8:30 na safiyar Gaza ne dai tsagaita wutar yakin ya fara aiki wanda ya yi daidai da karfe 6;30 agogin GMT.

Sai dai mutanen Gaza suna cikin dari-dari bisa sanayyarsu da halayyar HKI na rashin cika alkawali ko  aiki da wata yarjejeniya.

Mintuna kadan bayan fara aiki da tsagaita wutar yakin ne dai jiragen yakin HKI su ka kai wasu hare-hare a cikin yankin na Gaza.

Yarjejeniyar ta kunshi cewa zangon farko na aiwatar da ita zai dauki makwanni 6  da za a saki fursunoni 33 daga Gaza, yayin da ita kuma HKI za ta saki Falasdinawa 737.

Bugu da kari a cikin zangon na farko za a tattauna yadda zango na biyu zai kasance da zai  kunshi kawo karshen yaki baki daya,kamar yadda fira ministan kasar Katar Muhammad Bin Abdurrahma ali-Thani ya fada kwanaki kadan da su ka gabata.

A wannan tsakanin ne za a saki  sauran fursunonin HKI sannan kuma a fara maganar sake gina yankin Gaza  a mataki na 3 kuma na karshe.

Watanni 15 HKI ta dauka tana yin kisan kiyashi da na kare dangi a cikin fadin Gaza bisa cikakken goyon bayan Amurka da kuma taimakon makamanta da su ka kunshi bama-bamai da albarusai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments